# zaɓe, zaɓi, zaɓaɓɓe ## Ma'ana Wannan kalma "zaɓe" da "zaɓaɓɓe" ana magana ne game da idan an zaɓi wani mutum ya yi wani aiki na musamman ko domin ya cike wani gurbi. * Idan "an zaɓa" za a iya cewa "zaɓaɓɓe" domin ya karɓi wani abu, kamar a ce, "zaɓaɓɓe don rai na har abada" Wannan na nufin an zaɓe su domin su karɓi rai madawwami. * Wannan furcfaɗar "zaɓaɓɓen lokaci" ana nufin "lokacin da Allah ya ƙaiyada" ko "lokcin da aka shirya" domin wani abu ya faru. * Wannan kalma "zaɓe" za a iya fassarata da ma'ana haka "in an umarta" ko "asa" wani mutum ya yi wani aiki. Shawarwarin Fassara: * Ya danganta ga nassin, hanyoyin fassara "zaɓe" zai iya zama "zaɓi" ko "asa" ko "ƙuri'ar zaɓe" ko "wakilci." * Wannan kalma "zaɓaɓɓe" za a iya fassarawa ta zama "an sanya" ko "shirya" ko "zaɓaɓɓe musamman." * Wannan faɗar "an naɗa" za a iya fasara ta a ce "an zaɓa." Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * 1 Sama'ila 08:11 * Ayyukan Manzanni 03:20 * Ayyukan Manzanni 06:02 * Ayyukan Manzanni 13:48 * Farawa 41:33-34 * Littafin Lissafi 03:9-10