# Mai Iko Dukka ## Ma'ana Wannan kalma "Mai Iko Dukka" yana nufin "mai dukkan ƙarfi;" a cikin Littafi Mai Tsarki, a kowanne lokaci ana nufin Allah ne. * Wannan laƙabi "Mai Iko Dukka" ko "Wannan Mai Iko Dukka" ana nufin Allah ne kuma ya bayyana cewa yana da dukkan ƙarfi da iko bisa komai. * Wannan kalmar kuma akan yi amfani da ita a kwatanta Allah a cikin laƙabai masu nuna zatinsa , "Mai Iko Dukka Allah" ko "Allah Mai Iko Dukka" ko "Ubangiji Mai Iko Dukka" ko "Ubangiji Allah Mai Iko." Shawarwarin Fassara: * Wannan kalmar za a iya fassarata haka "Mai Dukkan Iko" ko "Mai Iko Gabaɗaya" ko "Allah, wanda shi ne mai ƙarfi gabaɗaya." * Hanyoyin fassara wannan faɗar "Ubangiji Allah Mai Iko Dukka" sune, "Allah, Mai Iko a Mulki" ko "Mai Iko Allah Makaɗaici" ko "Mai Girma Allah Ubangiji Mamallakin Komai." (Hakanan duba: Allah, ubangiji, iko) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Fitowa 06:2-5 * Farawa 17:01 * Farawa 35:11-13 * Ayuba 08:03 * Littafin Lissafi 24:15-16 * Wahayin Yahaya 01:7-8 * Rut 01:19-21