# zina, zinace-zinace, mazinaci, mazinaciya, mazinata ## Ma'ana Wannan kalma "zina" ma'anarta zunubi ne wanda mutum mai aure yake yi sa'ad da yana sha'anin kwana da wadda ba matarsa ko wanda ba mijinta ba. Zinace-zinace na nufin maimaita halin zina ko mutum mai yin wannan zunubi. * Ma'anar "mazinaci" shi ne namijin dake aikata zina. * Ma'anar "mazinaciya" shi ne matar aure musamman da take aikata zina. * Zina yana karya alƙawarin da miji da mata suka yiwa juna a aurensu. * Allah ya dokaci Isra'ilawa kada su yi zina. * Yawancin lokaci akan yi amfani da kalmar "zina" domin a nuna yadda mutanen Isra'ila suke yin rashin aminci wa Allah musamman sa'ad da suke wa gumaku sujada. Shawarwarin Fassara: * Idan yaren da suke fassara basu da kalma guda mai ma'anar "zina," za a iya fassara wa da faɗar haka, "yin jima'i da matar wani" ko "shafar abokin auren wani ko wata. * Wasu harsuna watakila suna da yadda suke fassara zina, misali "kwana da wanda ba matarka ko mijinki ba" ko kuma "yin rashin aminci ga matar mutum." * Sa'ad da aka yi amfani da "zina"a misali, zai fi kyau a fassara kai tsaye domin a nuna yadda Allah ke kallon mutanensa marasa biyayya idan aka kwatanta da abokin aure marar aminci. Idan wannan baiyi bayani ba sosai a yaren fassarar, amfani da misalin "zina" za a iya fassarawa a matsayin "rashin aminci" ko "lalata" ko "kamar abokin aure marar aminci." (Hakanan duba: aikata, alƙawari, lalatar zina, kwanciya da, aminci) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Fitowa 20:14 * Hosiya 04:1-2 * Luka 16:18 * Matiyu 05:28 * Matiyu 12:39 * Wahayin Yahaya 02:22