# zama 'ya'ya, maidawa 'ya'ya ## Ma'ana Wannan furci "zama 'ya'ya" yana nuna hanyar da wani bisa tsarin shari'a zai iya zama ɗan wasu mutane waɗanda ba su suka haife shi cikin jiki ba. * Littafi mai Tsarki ya yi amfani da "zama 'ya'ya" domin a misalta yadda Allah yake sa mutane su shigo cikin iyalinsa, ya sa cikin ruhaniya su zama 'ya'yansa maza da mata. * Waɗanda suka zama 'ya'ya, masu gaskatawa sun zama magãda tare da Yesu Almasihu, suna da dukkan 'yancin da 'ya'ya maza da mata na Allah suke da shi. Shawarwarin Fassara: * Wannan kalma za a iya fassara ta da irin furci da masu juyi zuwa yarensu suke amfani da ita su faɗi irin dangantakar dake musamman tsakanin iyaye da yaro. A tabbatar an gane cewa ana bada misali ne ko kuma ma'ana ne cikin ruhaniya. * Wannan furci "ɗanɗana zama 'ya'ya" za a iya juya shi ya zama, "Allah ya ɗauki wasu a matsayin 'ya'yansa" ko "'zama 'ya'yan (ruhaniya) na Allah." * A "jira zama 'ya'ya" za a iya fassarawa haka "a sa begen zama 'ya'ya" ko "a jiea da bege ga Allah ya karɓa a matsayin 'ya'ya." * Faɗar "maida su 'ya'ya" za a iya fassarawa haka "a karɓe su a matsayin 'ya'yansa" ko "a maida su 'ya'yansa na (ruhaniya)." (Hakanan duba: magãji, gãdo, ruhu) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Afisawa 01:5 * Galatiyawa 04:3-5 * Romawa 08:14-15 * Romawa 08:23 * Romawa 09:04