# hasala, huci, husata ## Ma'ana Hasala jin haushi ne na fitar hankali da ba za a iya tsai da shi ba. Sa'ad da mutum ya yi fushin fitar hankali, ma'ana wannan mutumin na bayyana haushinsa ta hanyar dake cutarwa. * Hasalar fitar hankali na faruwa ne sa'ad da tunanin sanin yakamata ya kuɓuce wa mutum har da bai iya riƙe kansa da yanayinsa ba. * kalmar "huci" na iya zama hurawa da ƙarfi, ana iya kwatanta shi da haukan ruwan teku mai "hauka." * Idan "al'ummai suka yi huci "a nan ne kuma mutane marasa tsoron Allah ke yi masa rashin biyayya da tayarwa. * A "cika da hasala" na nufin a yi ɗaukewa gabaɗaya da baƙinciki. (Hakanan duba: fuushi, kãme kai) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Ayyukan Manzanni 04:25 * Daniyel 03:13 * Luka 04:28 * Littafin Lissafi 25:11 * Littafin Misalai 19:03