# gofa ## Ma'ana Wannan kalma "gofa" wani irin itacen fir ne da yake da yawa a yankin da mutane ke zaune a lokacin Littafi Mai Tsarki, musamman ƙasashen dake gaɓas da Tekun Baharmaliya. * Sifrus da Lebanon wurare ne biyu da Litttafi Mai Tsarki ya ambace su musamman suna da itatuwan gofa da yawa. * Katakan da Nuhu ya gina jirgi mai yiwuwa na gofuna ne. * Saboda itacen gofa yana da kauri ga iya daɗewa, mutanen dã sun yi amfani da su domin gina kwale kwale da kuma wasu gine gine. (Hakanan duba: akwati, Sifuros, itacen fir, Lebanon) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Ayyukan Manzanni 11:19-21 * Farawa 06:14 * Hosiya 14:08 * Ishaya 44:14 * Ishaya 60:13 * Zakariya 11:02