# Yahaya Markus ## Gaskiya Yahaya Markus, wanda kuma aka fi sani da suna "Markus," yana ɗaya daga cikin waɗanda suka yi tafiya tare da Bulus a cikin tafiye-tafiyensa na bishara. Lallai an nuna cewa shine marubucin Littafin Bishara ta Markus. * Yahaya Markus ya raka ɗan'uwansa Barnabas tare da Bulus a fitarsu ta farko tafiya bishara. * Sa'ad da aka sanya Bitrus cikin kurkuku a Urshalima, masubi na wurin suka yi addu'a dominsa a cikin gidan mahaifiyar Yahaya Markus. * Markus ba manzo ba ne, amma ya sami koyarwa daga su Bulus da Bitrus ya kuma yi aiki tare da su cikin hidima. (Hakanan duba: Barnabas, Bulus) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * 2 Timoti 04:11-13 * Ayyukan Manzanni 12:24-25 * Ayyukan Manzanni 13:05 * Ayyukan Manzanni 13:13 * Ayyukan Manzanni 15:36-38 * Ayyukan Manzanni 15:39-41 * Kolosiyawa 04:10-11