# Hannatu ## Gaskiya Hannatu ita ce mahaifiyar annabi Sama'ila. Ita ɗaya ce daga cikin matan Elkana guda biyu. * Hannatu bata iya samun damar haihuwa ba, wanda abin ya zama abin baƙin ciki a gare ta. * A cikin haikali, Hannatu ta yi addu'a da gaskiya domin Allah ya bata ɗa tare da alƙawarin zata miƙa wanan ɗa a bautar Allah. * Allah ya amsa addu'arta da kuma yaron nan Sama'ila ya yi girma sai ta kawo shi ya yi hidima a cikin haikali. * Bayan haka Allah ya ba Hannatu waɗansu 'ya'ya bayan Sama'ila. (Hakanan duba: ɗaukan ciki, Sama'ila) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * 1 Sama'ila 01:1-2 * 1 Sama'ila 02:1