# Bafarisiye, Farisawa ## Ma'ana Farisawa mahimman mutane ne ƙungiya kuma mai iko na shugabanin addinin Yahudawa a zamanin Yesu. * Da yawansu mawadatan tsaka-tsaka ne 'yan kasuwa wasunsu kuma firistoci ne. * Cikin dukkan shugabannin Yahudawa, Farisawa sune masu matsawa ayi biyayya da Shari'ar Musa da kuma wasu dokokin Yahudawa da al'adunsu. * Suna da damuwar su ga mutanen Yahudawa sun keɓe daga cuɗanya da al'umman dake kewaye da su. Sunan nan "Bafarisiye ya zo ne daga wannan magana "keɓewa." * Farisawa sun gaskata akwai rayuwa bayan an mutu; kuma sun gaskata akwai mala'iku da wasu hallitun ruhohi. * Farisawa da Sadusiyawa sun ƙalubalanci Yesu da Kiristocin fãri. (Hakanan duba: majalisa, shugabannin Yahudawa, shari'a, Sadusiyawa) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Ayyukan Manzanni 26:04 * Yahaya 03:1-2 * Luka 11:44 * Matiyu 03:07 * Matiyu 05:20 * Matiyu 09:11 * Matiyu 12:02 * Matiyu 12:38 * Filibiyawa 03:05