# Maɗaukaki ## Ma'ana Wannan furci "Maɗaukaki" sunan naɗi ne na Allah. Ana nufin girmansa da ikonsa. * Ma'anar wannan furci ya yi kama da "Marar Takwara" ko Mafifici Dukka." * Wannan kalma "sama" a cikin sunan nan ba ana nufin tsayin jiki ne ba ko nisa. Ana nufin girmansa. Shawarwarin Fassara: * Wannan furci za a iya fassara shi haka "Allah na Sama" ko "Mai Dukka" ko "Allah Maɗaukaki" ko "Babban nan" ko "Mafificin nan" ko "Allah" wanda Ya Fi Kowa." * Idan an yi amfani da "na sama" ba wai ana nufin tsayin jiki ko dogo ba. (Hakanan duba: Allah) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Ayyukan Manzanni 07:47-50 * Ayyukan Manzanni 16:16-18 * Daniyel 04:17-18 * Maimaitawar Shari'a 32:7-8 * Farawa 14:17-18 * Ibraniyawa 07:1-3 * Hosiya 07:16 * Littafin Makoki 03:35 * Luka 01:32