Menene Yesu ya ce mutane biyu, wato mata da miji sukan zama a lokacin da sun yi aure?
Yesu ya ce mutanen nan biyu su na zama jiki daya.
Menene Yesu ya ce game da abin da Allah ya haɗa tare a cikin aure?
Yesu ya ce duk abin da Allah ya haɗa tare, kada wani mutum ya raba.