# Menene firist ke sa domin ya cire toka daga bagadin? Firist zai sanya rigunansa na lilin, zai kuma sa ƙananan kaya 'yan ciki na lilin don ya kwashe tokar a bagadin. # Menene firist din zai yi kafin ya fitar da tokar daga cikin zango? Zai tuɓe rigunansa ya sa wasu rigunan domin ya kai tokar bayan zango a wuri mai tsabta.