# Ga menene magudanar ruwa zai zama wanda ke a buɗe wa gidan Dauda a wannan ranar? Magudanar ruwar zai zama na zunubansu da rashin tsarkinsu. # Menene Yahweh zai datse daga ƙasar kuma don menene? Yahweh zai datse sunayen gumaka daga ƙasar don kada a ƙara tunawa da su. # Menene Yahweh zai sa su fita daga ƙasar? Yahweh zai sa annabawan ƙarya da ƙazamin ruhunsu su fita daga ƙasar.