# Bayan da Haruna yayi baye-bayen kamar yadda Musa ya ce a yi, Menene Haruna yayi wa mutanen? Bayan da Haruna yayi baye-bayen, ya daga hannunsa ya albarkace mutanen. # Menene ya faru sa'adda ɗaukakar Yahweh ya bayyana wa mutanen? Sa'adda ɗaukakar Yahweh ya bayyana wa mutanen,wuta ta fito ta cinye baikon ƙonawar da kitsen dake kan bagadin. # Menene mutanen suka yi sa'adda wutan ta fito daga Yahweh? Sa'adda wutan ta fito daga Yahweh, sai mutanen suka yi ihu suka kwanta fuskokinsu a ƙasa.