# Wanene suka zo wurin Ezekiyel don su tambaye shi? Dattawan Isra'ila ne suka zo wurin Ezekiyel don su tambaye shi. # Me yasa Yahweh yayi tambaya ko ya kamata mutanen su roke shi? Yahweh yace saboda dattawan sun É—auki gunmakan su a zuciyar su.