# Menene Diyotarifis ke kauna? Diyotarifis ya na kaunar ya zama shine farko a cikin ikklisiya. # Menene halin Diyotarifis zuwa ga Yahaya? Diyotarifis bai karɓi Yahaya ba. # Menene Yahaya zai yi idan ya zo wurin Gayus da kuma ikklisiyar? Idan Yahaya ya zo zai yi tuna da mugun halayen Diyotarifis # Menene Diyotarifis ya ke yi da yan'uwan da suke fita domin Sunan? Diyotarifis ba ya karɓan yan'uwan. # Menene Diyotarifis ya ke yi da waɗanda suka karbi yan'uwa da ke fita domin Sunan? Diyotarifis ya na hana su karɓan yan'uwan, ya na kuma korar su da ga ikkklisiya.