# Abincin da muke ci na sa mu karu ne ko ragu ga Allah? Abinci ba zai bamu tagomashi a wurin Allah ba. Ko mun ci, bamu kara karbuwan mu ba, ko ba mu ci ba, ba mu rage karbuwan mu ba. # Menene za mu yi lura cewa kada 'yancinmu ya zama? Mu yi hatara kada 'yancin mu ya zama sanadiyar tuntuben wani mai rarraunar bangaskiya.