# Da wanene Bulus ke nufin kada masubi na Korontiyawa su yi hudda ? Ya na nufin cewa kada su yi hudda da duk wanda ake kira ɗan'uwa amma yana zama cikin fasikanci, ko zari, ko bautar gumaka, ko yin ashar, ko mashayi, ko ɗan'damfara. # Wanene ya kamata masubi za su shar'anta? Ya kamata su shar'anta waɗanda suke cikin ikilisiya . # Wanene ke shar'anta waɗanda suke wajen Ikilisiya? Allah ke shar'anta waɗanda ke wajen Ikilisiya.