# waɗanda suke shakka "waɗanda har yanzu basu yarda da cewa Yesu Allah bane" # kuna fisgo su daga wuta Bayanin nan na nuna yadda ake jawo mutane daga wuta kafin su fara ƙonewa. AT: "ana yi masu duk abin da yakamata domin a tserar da su daga mutuwa da rashin sannin Almasihu. Wannan na kama da ana jawosu ne daga cikin wuta" (Dubi: [[rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor]]) # Ga waɗansu kuma ku nuna jinƙai da rawar jiki "Ku nuna jinƙai ga jama'a, amma ku yi tsoron zunubi kamar yadda suka yi" # Kuyi kyamar koda tufafin jikinsu ma Yahuza yana zuguiguita al'amarin don ya gargaɗi masu karatun cewa zasu iya zama kamar waɗannan masu zunubi. AT: "Ku yi da su kamar kuma zaku iya zama masu laifin zunubi tawurin taɓa tufafinsu" (Dubi: [[rc://*/ta/man/translate/figs-hyperbole]])