[ { "title": "mulkoki suka girgiza", "body": "Anan, kalmar \"girgiza\" ita ce kalmar da marubucin yayi amfani da ita a Zabura 46:1 don bayyana tasirin girgizar ƙasa a kan duwatsu. Marubucin yayi maganar kifar da\nmulkoki da dakaru kamar girgizar kasa zata hallaka su. Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: \"rundunoni sun kifar da masarautu\" (Duba: figs_metaphor da figs_activepassive)" }, { "title": "ya tayar da muryarsa", "body": "\"Allah ya daga murya.\" Marubucin yayi magana akan \"murya\" a matsayin abun da mutum zai\niya ɗauka ya ɗaga sama. Wannan yana nufin cewa muryar ta ƙara ƙarfi. AT:\n\"Allah ya yi ihu\" (Duba: figs_ metaphor)" }, { "title": "Allah na Yakubu shi ne mafakarmu", "body": "Marubucin yayi magana game da Allah kamar dai shine wurin da mutane zasu iya zuwa don\naminci. AT: \"Allah na Yakubu yana bamu aminci\" (Duba: figs_metaphor)" } ]