[ { "title": "Wane ne zai haura tsaunin ... wurinsa mai tsarki?", "body": "Duk waɗannan tambayoyin suna nufin abu ɗaya ne. Mai magana yana tambaya game da\nwanda aka yarda ya je ya bauta wa Yahweh. (Duba: figs_parallelism)" }, { "title": "tsaunin Yahweh", "body": "Wannan yana nufin Tsaunn Sihiyona a Yerusalem." }, { "title": "da hannuwa masu tsarki", "body": "Kalmar nan “hannu” tana wakiltar abin da mutum yake yi. Don “hannayensa” su zama masu tsabta yana nufin ya yi abin da yake dai-dai. AT: \"wanda ya aikata abin da yake\ndai-dai\" (Duba: figs_metonymy)" } ]