[ { "title": "Yahweh makiyayina ne", "body": "Marubucin yayi magana game da Yahweh kamar makiyayi. Wannan ya nanata yadda Allah yake kulawa da mutane kamar yadda makiyayi yake kulawa da tumakinsa. AT: \"Yahweh kamar makiyayi ne a gareni\" ko \"Yahweh yana kula da ni kamar yadda makiyayi ke kula da tumakinsa\" (Duba: figs_metaphor)" }, { "title": "ba zan rasa komai ba", "body": "Ana iya bayyana wannan a cikin tsari mai kyau. AT: \"Ina da duk abin da nake\nbuƙata\" (Duba: figs_litotes)" }, { "title": "Yana sa ni in kwanta a cikin korayen makiyayu", "body": "Marubucin yana magana ne game da kansa kamar tunkiya, kuma yana magana game da\nYahweh kamar makiyayi. AT: \"Yana ba ni hutawa kamar makiyayi wanda ke jagorantar tumakinsa don hutawa a cikin makiyaya masu ciyayi\" (Duba: figs_metaphor)" }, { "title": "yana bi da ni kurkusa da kwantaccen ruwa", "body": "Marubucin yana magana ne game da kansa kamar tunkiya, kuma yana magana game da\nYahweh kamar makiyayi. AT: \"yana tanadar min da abin da nake buƙata kamar makiyayi wanda ke jagorantar tumakinsa a gefen ruwa mai nutsuwa\" (Duba: figs_metaphor)" } ]