[ { "title": "Mahadin Zance:", "body": "Yahweh yana ci gaba da magana da sabon sarkin Isra'ila." }, { "title": "yankunan duniya", "body": "\"ƙasashen da suke da nisa sosai\"" }, { "title": "Za ka mallake su da sandar ƙarfe", "body": "An yi magana akan cin al'ummai kamar ya fasa su, kuma ana maganar ƙarfinsa kamar sandar ƙarfe. AT: \"Za ku kayar da su kwata-kwata da ƙarfinku\" (Duba: figs_metaphor)" }, { "title": "za ka ragargaza su su farfashe", "body": "An yi maganar al'umman da ke hallakarwa kamar za a farfashe su kamar tukunyar yumɓu. AT: za ku hallakar da su kwata-kwata kamar tukunyar yumɓu \"(Duba: figs_metaphor da figs_simile)" } ]