[ { "title": "Kun bada bakinku ga mugunta", "body": "Allah yana magana akan mutumin da yake faɗar mugayen abubuwa kamar dai bakin mutumin saƙo ne wanda mutumin yake aikawa don aikata mugunta. AT: \"Kullum kuna\nfaɗin mugunta\" (Duba: figs_metaphor da figs_synecdoche)" }, { "title": "kuma harshenku na fitar da ruɗu", "body": "Kalmar \"harshe\" tana wakiltar mutumin da yake magana. AT: \"Kullum kuna yin\nƙarya\" (Duba: figs_synecdoche)" }, { "title": "Ka zauna kana magana gãba da ɗan'uwanka; ka na saran ɗan mahaifiyarka", "body": "Waɗannan jimlolin guda biyu suna da ma'ana iri ɗaya amma suna amfani da kalmomi daban-daban. Allah ya zarge su da yin ƙarya game da danginsu. (Duba: figs_parallelism)" } ]