[ { "title": "Bari mutuwa ta afko masu", "body": "Ana maganar mutuwa kamar mutum ne da zai iya afkawa mutane. AT: \"Bari\nmaƙiyana su mutu farat ɗaya\" (Duba: figs_personification)" }, { "title": "gama mugunta ce kaɗai rayuwarsu", "body": "Ana maganar mugunta kamar abu ne wanda zai iya kasancewa a wani wuri. Maganar muguntar da magabtansa suka saba magana ana maganarsu kamar mugunta tana tare da su ko kuma\nkusa da su. AT: \"koyaushe suna aikata mugunta a inda suke zaune\" (Duba: figs_metaphor)" } ]