[ { "title": "dukkan zurfafan teku", "body": "Wannan jimla na gabatad da kowane hallita da ke zaune cikin zurfafan tekuna. AT: \"dukkan hallitu cikin zurfafan teku\" (Dubi: figs_metonymy)" }, { "title": "wuta da ƙanƙara, dusar ƙanƙara da giza-gizai, iskar hadari", "body": "Marubuci yana magana da waɗannan abin aukuwa bisa ga ikon Allah sai ka ce su mutane ne da kuma dokokinsu su yabe Yahweh. (Dubi: figs_personification)" }, { "title": "iskar hadari masu biyayya da maganarsa", "body": "Jimla \"maganarsa\" na gabatad da abin da Yahweh ya umurta. AT: \"iskar hadari da ke yin abin da Yahweh ya umurta\" (Dubi: figs_metonymy)" } ]