[ { "title": "Oh, dama ceton Isra'ila zai zo daga Sihiyona!", "body": "Wannan kirari ne. Marubucin yana fadar abin da yake so ko kuma fatan Allah ya yi. AT: \"Ina fatan dai ceton Isra'ila ya zo daga Sihiyona!\" (Duba: figs_metonymy)" }, { "title": "Yakubu zai yi murna, Isra'ila ma zata yi farinciki", "body": "Waɗannan jimlolin guda biyu suna nufin abu ɗaya. Anan dukka \"Yakubu\" da \"Isra'ila\" suna\nwakiltar mutanen Isra'ila. Za a iya haɗa jimloli biyu a cikin fassarar. AT: \"to duk\njama'ar Isra'ila za su yi murna ƙwarai\" (Duba: figs_parallelism da figs_synecdoche)" } ]