rachelua_ha_isa_tn_l3/33/10.txt

14 lines
1.1 KiB
Plaintext

[
{
"title": "Yanzu ne za a ɗagani sama; yanzu za a fifita ni",
"body": "Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. Waɗannan jimlolin guda biyu suna da ma'ana iri ɗaya\nkuma suna nanata cewa ana ɗaukaka Yahweh. AT: \"yanzu zan daukaka kaina\nkuma na nuna cewa na cancanci kowa ya girmama ni\" (Duba: figs_activepassive da figs_parallelism)"
},
{
"title": "Kun ɗauki cikin ƙai-ƙai, kun haifi ciyawa",
"body": "Wannan yana maganar Asiriyawa suna yin shiri kamar suna daukar ciki kuma suna haihuwar\nshirinsu kamar yadda uwa take haihuwar jariri. Wannan yana magana ne game da shiryeshiryensu\nmarasa amfani ta hanyar kwatanta su da ƙaiƙayi. AT: \"Kuna yin shiryeshiryen\nda ba su da amfani kamar ƙaiƙayi da ciyawa\" (Duba: figs_metaphor)"
},
{
"title": "Mutanen za a ƙona su su zama danƙo, kamar yadda a ke sassare sarƙaƙƙiya a ƙone ta",
"body": "Wannan yana kwatanta yadda mutane za a kone gawawwakin kamar yadda ake kona ƙaya.\nHaka nan, ana iya bayyana wannan a cikin sigar aiki. AT: \"Wuta za ta ƙone\nmutane gawarwakin zuwa lemun tsami kamar yadda manomi yana sare ƙaya kuma ya ƙone\nsu \"(Duba: figs_simile da figs_activepassive)"
}
]