[ { "title": "Muhimmin Bayani:", "body": "Yahweh ya ci gaba da magana da mutanen Isra'ila da Yerusalem." }, { "title": "abin da ban taɓa yi ba da kuma irin wanda ba zan sake yin irin sa ba", "body": "\"kamar yadda ban taɓa yi ba kuma ba zan sake yi a irin wannan hanyar ba\" ko \"kamar yadda\nban taɓa yi ba kuma ba zan taɓa yi ba\"." }, { "title": "ubanni za su ci naman 'ya'yansu, 'ya'ya kuma za su ci naman iyayensu", "body": "Wataƙila Ezekiyel yana faɗin abin da gaske zai faru idan mutane ba su da abinci." }, { "title": "kuma watsar da dukkanku da kuka rage ko ina", "body": "\"Zan tilasta dukkanku da kuka rage zuwa wurare daban-daban.\"" } ]